Kamar yadda Kamfanin Dillancin Labaran Hauza ya ruwaito, ana gabatar da jerin tattaunawa kan Mahdawiyya mai taken "Zuwa Ga Al'umma Mai Manufa", da nufin yada koyarwa da ilimin da ke da alaka da Imam al-Mahdi (Allah ya gaggauta bayyanarsa), ga ku masu karatu.
Aya Ta Biyu
«وَنُریدُ أنْ نَمُنّ عَلَی الّذینَ اسْتُضْعِفُوا فِی الارْضِ وَنَجْعَلَهُمْ أئمّْة وَنَجْعَلَهُمُ الْوارِثینَ.»
“Kuma Mun so Mu yi falala ga wadanda aka raunana a cikin kasa, kuma Mu sanya su shugabanni, kuma Mu sanya su magada.” (Suratul Qasas, Aya ta 5)
Wannan aya, kamar yadda Imam Ali (A.S) ya fada a cikin *Nahjul Balagha* da kuma wasu hadisai da dama da aka ruwaito daga sauran Imamai (A.S), tana nuni ne ga nasarar wadanda aka raunana a kan masu girman kai, da kuma cewa a karshe, duniya za ta kasance a hannun mutanen kirki masu adalci.
Wannan aya ba ta magana kawai a kan wani takamaiman shiri na musamman da ya shafi Bani Isra'ila ba; a'a, tana bayyana wata ka'ida ce ta gaba daya ga dukkan zamani da shekaru. Wannan bushara ce ta musamman game da nasarar gaskiya a kan karya, da kuma imani a kan kafirci. Misali mafi cika na wannan a baya shi ne gwamnatin Annabin Musulunci (S.A.W.A) da sahabbansa bayan bayyanar Musulunci.
To amma, misali mafi girma kuma mafi fadi na wannan aya shi ne bayyanar gwamnatin gaskiya da adalci a daukacin fadin duniya a hannun Hazrat Imam Mahdi (A.F).
Wannan aya tana daya daga cikin ayoyin da ke yin bushara a fili game da "bayyanar" irin wannan gwamnati; shi ya sa Ahlul Bait (A.S) suka yi ishara da wannan babbar bayyanar a lokacin da suke tafsirinta. An ruwaito daga Imam Ali (A.S) a cikin *Nahjul Balagha*:
«لَتَعْطِفَنَّ الدُّنْیا عَلَینَا بَعْدَ شِمَاسِهَا عَطْفَ الضَّرُوسِ عَلَی وَلَدِهَا وَ تَلَا عَقِیبَ ذَلِکَ "وَ نُرِیدُ أَنْ نَمُنَّ عَلَی الَّذِینَ اسْتُضْعِفُوا فِی الْأَرْضِ وَ نَجْعَلَهُمْ أَئِمَّةً وَ نَجْعَلَهُمُ الْوارِثِینَ".»
“Duniya za ta karkato zuwa gare mu bayan taurin kanta da bijirewarta — kamar yadda taguwa mai taurin kai take karkata ga danta domin shayar da shi — sannan ya karanta wannan aya: 'Kuma Mun so Mu yi falala ga wadanda aka raunana a fadin kasa...'” (Nahjul Balagha, Hikima ta 209)
A cikin wani hadisin na daban, Imam Ali (A.S) yana cewa a tafsirin wannan aya:
«هُمْ آلُ مُحَمَّدٍ یبْعَثُ اللَّهُ مَهْدِیهُمْ بَعْدَ جَهْدِهِمْ فَیعِزُّهُمْ وَ یذِلُّ عَدُوَّهُمْ.»
“Su ne Aali Muhammadu (iyalan gidan Muhammadu), Allah zai tayar da Mahdinsu bayan tsanani da matsin lamba da suka sha, sai ya daukaka su kuma ya wulakanta makiyansu.” (Sheikh Tusi, Kitabul Ghaibah, shafi na 184)
Wannan tattaunawa za ta ci gaba...
An ɗauko daga littafin "Darsnameh Mahdaviyyat" na Khodamurad Salimiyan tare da dan gyara kadan
Ra'ayinka